7 Da wasiƙar ta iso wurinsu, sai suka kwashi 'ya'yan sarki guda saba'in, suka karkashe su. Suka sa kawunansu cikin kwanduna, suka aika wa Yehu a Yezreyel.
8 Da aka faɗa masa cewa an kawo kawunan 'ya'yan sarki, sai ya ce, “Ku ajiye su kashi biyu a ƙofar garin har safiya.”
9 Da safe, sa'ad da ya fita, ya tsaya, sai ya ce wa mutane duka, “Ba ku da laifi, ni ne na tayar wa maigidana har na kashe shi, amma wane ne ya kashe dukan waɗannan?
10 Ku sani fa ba maganar da Ubangiji ya faɗa a kan gidan Ahab da ba za ta cika ba, gama Ubangiji ya aikata abin da ya faɗa ta bakin bawansa Iliya.”
11 Haka kuwa Yehu ya karkashe waɗanda suka ragu na gidan Ahab a Yezreyel, wato dukan manyan mutanensa, da abokansa, da firistocinsa. Bai rage masa ko guda ba.
12 Yehu kuma ya fita zai tafi Samariya. A hanya, sa'ad da yake a Bet-eked ta makiyaya,
13 sai ya sadu da 'yan'uwan Ahaziya Sarkin Yahuza, sai ya ce, “Ku su wane ne?”Sai suka amsa, “Mu 'yan'uwan Ahaziya ne, mun zo mu gai da 'ya'yan sarki ne da 'ya'yan sarauniya.”