9 Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji kamar yadda kakanninsa suka yi. Bai rabu da zunuban Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa mutanen Isra'ila su yi zunubi.
10 Shallum ɗan Yabesh ya ƙulla masa maƙarƙashiya, ya buge shi a Ibleyam, ya kashe shi, sa'an nan ya hau gadon sarautarsa.
11 Sauran ayyukan da Zakariya ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila.
12 Wannan shi ne alkawarin da Ubangiji ya yi wa Yehu, cewa 'ya'yansa maza za su zauna a gadon sarautar Isra'ila har tsara ta huɗu. Haka kuwa ya zama.
13 Shallum ɗan Yabesh ya ci sarauta a shekara ta talatin da tara ta sarautar Azariya Sarkin Yahuza. Ya yi mulki wata ɗaya a Samariya.
14 Menahem ɗan Gadi daga Tirza ya zo Samariya ya bugi Shallum ɗan Yabesh a Samariya, ya kashe shi, ya hau gadon sarautarsa.
15 Sauran ayyukan Shallum duk da makircin da ya ƙulla, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila.