13 Ina Sarkin Hamat, da Sarkin Arfad, da sarkin birnin Sefarwayim, da Sarkin Hena, da Sarkin Iwwa?”
14 Hezekiya ya karɓi wasiƙa daga hannun manzannin ya karanta ta, sa'an nan ya shiga Haikalin Ubangiji, ya buɗe ta, ya ajiye ta a gaban Ubangiji.
15 Sa'an nan ya yi addu'a ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji Allah na Isra'ila, kai da kake zaune a kan gadon sarautarka, kai kaɗai ne Allah a dukan mulkokin duniya, kai ne ka yi sama da ƙasa.
16 Ka kasa kunne, ya Ubangiji, ka yi. Ka buɗe idanunka, ya Ubangiji, ka gani, ka kuma ji irin maganar Sennakerib wadda ya aiko don a yi wa Allah mai rai ba'a.
17 A gaskiya kam, ya Ubangiji, sarakunan Assuriya sun lalatar da al'ummai da ƙasashensu.
18 Sun jefar da gumakansu cikin wuta, gama su ba Allah ba ne, amma ayyukan hannuwan mutane ne, waɗanda aka yi da itace da dutse, saboda haka an iya a hallaka su.
19 Yanzu ya Ubangiji Allahnmu, ina roƙonka ka cece mu daga hannunsa domin dukan mulkokin duniya su sani kai kaɗai ne Allah, ya Ubangiji.”