21 Da Sarkin Isra'ila ya gan su, sai ya ce wa Elisha, “Ya mai girma, in karkashe su? In karkashe su?”
22 Amma Elisha ya ce, “Ba za ka karkashe su ba. Ba za ka karkashe waɗanda ba kai ka kama su ta wurin takobinka ko bakanka ba. Ka ba su abinci da ruwa su ci su sha, su koma wurin shugabansu.”
23 Sai ya shirya musu babbar liyafa. Sa'ad da suka ci suka sha, sai ya sallame su, suka koma wurin shugabansu. Suriyawa kuwa ba su ƙara kai wa ƙasar Isra'ila hari ba.
24 Bayan wannan kuwa Ben-hadad, Sarkin Suriya, ya tattara sojojinsa duka, ya haura ya kewaye Samariya da yaƙi.
25 Aka yi yunwa mai tsanani a Samariya a lokacin da aka kewaye ta da yaƙin, har aka riƙa sayar da kan jaki a bakin shekel tamanin, an kuma sayar da rubu'in mudu na kashin kurciya a bakin shekel biyar.
26 Sa'ad da Sarkin Isra'ila yake wucewa ta kan garun birni, sai wata mace ta yi masa kuka, ta ce, “Ka yi taimako, ran sarki ya daɗe.”
27 Shi kuwa ya ce, “Idan Ubangiji bai taimake ki ba, ƙaƙa zan yi, ni in taimake ki? Ina da alkama ne ko kuwa ina da ruwan inabi?