24 Bayan wannan kuwa Ben-hadad, Sarkin Suriya, ya tattara sojojinsa duka, ya haura ya kewaye Samariya da yaƙi.
25 Aka yi yunwa mai tsanani a Samariya a lokacin da aka kewaye ta da yaƙin, har aka riƙa sayar da kan jaki a bakin shekel tamanin, an kuma sayar da rubu'in mudu na kashin kurciya a bakin shekel biyar.
26 Sa'ad da Sarkin Isra'ila yake wucewa ta kan garun birni, sai wata mace ta yi masa kuka, ta ce, “Ka yi taimako, ran sarki ya daɗe.”
27 Shi kuwa ya ce, “Idan Ubangiji bai taimake ki ba, ƙaƙa zan yi, ni in taimake ki? Ina da alkama ne ko kuwa ina da ruwan inabi?
28 Me yake damunki?”Sai ta amsa, ta ce, “Wannan mace ta ce mini, in kawo ɗana mu ci yau, gobe kuma mu ci nata.
29 Sai muka dafa ɗana muka cinye. Kashegari kuwa na ce mata ta kawo ɗanta mu ci, amma sai ta ɓoye shi.”
30 Da sarki ya ji maganar macen, sai ya keta tufafinsa, sa'ad da yake wucewa ta kan garun birni. Sai mutane suka gani, ashe, yana saye da rigar makoki a ciki.