3 Za a kwashe ku, a fitar da kuTa inda garu ya tsage na mafi kusaduka, a jefar.”
4 Ubangiji ya ce,“Jama'ar Isra'ila,Ku tafi Betel, tsattsarkan wuri,Ku yi ta zunubi!Ku tafi Gilgal ku ƙara zunubi!Ku yi ta kawo dabbobi sadakakowace safiya.A kowace rana ta ukuKu yi ta ba da zaka.
5 Ku miƙa abincinku hadaya tagodiya.Ku yi ta yin fariya da hadayarku tayardar rai!Gama irin abin da kuke jin daɗin yike nan.”
6 Ubangiji ya ce,“Ai, ni ne, na sa a yi yunwa abiranenku.Shi ya sa ba ku da abinci.Duk da haka ba ku juyo gare ni ba.
7 Na hana wa shuke-shukenku ruwaA lokacin da suka fi bukata.Na sa a yi ruwa a wani birni,A wani birni kuwa na hana,Wata gonar ta sami ruwan sama,Amma wadda ba ta samu ba tabushe.
8 Ƙishirwa ta sa jama'a su tafke harbirane biyu ko ukuSuka tafi neman ruwa a birnin dasuke maƙwabtaka da shi,A nan ma ba su sami isasshen ruwansha ba,Duk da haka ba ku komo wurinaba.
9 “Na sa darɓa, da domanaSu lalatar da amfanin gonakinku.Fāra kuma ta cinye lambunankuDa gonakin inabinku, da itatuwanɓaurenku,Da na zaitun ɗinku.Duk da haka ba ku komo wurina ba.