10 Kamannin fuskokinsu, su huɗu ɗin, kowannensu yana da fuska irin ta mutum a gaba, da fuska irin ta zaki a dama, da fuska irin ta bijimi a hagu, da fuska irin ta gaggafa a baya.
11 Suka kuma buɗe fikafikansu sama. Kowane taliki yana taɓa fiffiken ɗan'uwansa da fikafikansa biyu, da kuma fikafikansa biyu yake rufe jikinsa.
12 Kowannensu kuwa ya miƙe gaba sosai, zuwa inda ruhu ya bishe shi. Sun tafi ba waiwaye.
13 A tsakiyar talikan akwai wani abu mai kama da garwashin wuta, kamar jiniyoyi kuma suna kai da kawowa a tsakanin talikan, wutar kuwa tana haskakawa. Daga cikin wutar kuma, sai ga walƙiya tana fitowa.
14 Talikan kuma suka yi ta giftawa suna kai da kawowa kamar walƙiya.
15 Da na dubi talikan, sai na ga ƙafafu huɗu kamar na keke a ƙasa kusa da talikan. Ɗaya domin kowane taliki.
16 Ga kamannin ƙafafun da yadda aka yi su. Suna ƙyalƙyali kamar duwatsu masu daraja. Dukansu huɗu fasalinsu ɗaya ne. An yi su kamar wata ƙafa tana cikin wata ƙafa.