7 Ƙafafunsu miƙaƙƙu ne, tafin sawayensu yana kama da na maraƙi, suna walƙiya kamar gogaggiyar tagulla.
8 Suna kuma da hannuwa kamar na mutane a ƙarƙarshin fikafikansu huɗu. Ga yadda fuskoki da fikafikan talikai huɗu ɗin suke.
9 Fikafikansu suna taɓa juna, kowannensu ya miƙe gaba, ba su juyawa sa'ad da suke tafiya.
10 Kamannin fuskokinsu, su huɗu ɗin, kowannensu yana da fuska irin ta mutum a gaba, da fuska irin ta zaki a dama, da fuska irin ta bijimi a hagu, da fuska irin ta gaggafa a baya.
11 Suka kuma buɗe fikafikansu sama. Kowane taliki yana taɓa fiffiken ɗan'uwansa da fikafikansa biyu, da kuma fikafikansa biyu yake rufe jikinsa.
12 Kowannensu kuwa ya miƙe gaba sosai, zuwa inda ruhu ya bishe shi. Sun tafi ba waiwaye.
13 A tsakiyar talikan akwai wani abu mai kama da garwashin wuta, kamar jiniyoyi kuma suna kai da kawowa a tsakanin talikan, wutar kuwa tana haskakawa. Daga cikin wutar kuma, sai ga walƙiya tana fitowa.