17 “Saboda haka ka ce, ‘Ni Ubangiji na ce, zan tattaro ku daga cikin al'ummai, da ƙasashen da aka warwatsa ku, ni kuwa zan ba ku ƙasar Isra'ila.’
18 Sa'ad da suka koma a ƙasar za su kawar da dukan abin da ya ƙazantar da ita, da dukan irin abar ƙyama da take cikinta.
19 Zan ba su zuciya ɗaya, in kuma sa sabon ruhu a cikinsu. Zan kawar musu da zuciya ta dutse, in ba su zuciya mai taushi,
20 domin su kiyaye dokokina, da ka'idodina, su aikata su. Za su zama mutanena, ni kuwa zan zama Allahnsu.
21 Amma waɗanda zuciyarsu ta karkata zuwa ga bin ƙazantattun abubuwa masu banƙyama, zan sāka musu gwargwadon ayyukansu, ni Ubangiji na faɗa.”
22 Sa'an nan kerubobin suka ɗaga fikafikansu tare da ƙafafunsu. Ɗaukakar Ubangiji kuwa tana bisa kansu.
23 Sai ɗaukakar Ubangiji ta bar tsakiyar birni, ta tsaya a bisa kan dutse wanda yake wajen gabas da birnin.