26 Kin yi karuwanci da Masarawa, maƙwabtanki masu kwaɗayi. Kin yawaita karuwancinki don ki tsokani fushina.
27 “Domin haka na miƙa hannuna gāba da ke, na rage rabonki, na ba da ke ga abokin gābanki masu haɗama, 'yan matan Filistiyawa waɗanda suka ji kunya saboda halinki na lalata.
28 “Kin kuma yi karuwanci da Assuriyawa domin ba ki ƙoshi ba. Kin yi karuwanci da su duk da haka ba ki ƙoshi ba.
29 Kin yawaita karuwancinki da Kaldiya, ƙasar ciniki, duk da haka ba ki ƙoshi ba.
30 “Kin cika uzuri,” in ji Ubangiji Allah. “Duba, kin aikata waɗannan abubuwa duka, ayyuka na karuwa marar kunya.
31 Kin gina ɗakunan tsafi a kowane titi da kowane fili. Amma ke ba kamar karuwa ba ce, da yake ba ki karɓar kuɗi.
32 Ke mazinaciyar mace, mai kwana da kwartaye maimakon mijinki!