41 Zan karɓe ku kamar turare mai ƙanshi sa'ad da na fisshe ku daga cikin sauran mutane, na tattaro ku daga ƙasashen da aka warwatsa ku. Zan nuna tsarkina a cikinku a idon sauran al'umma.
42 Za ku sani ni ne Ubangiji sa'ad da na kawo ku ƙasar Isra'ila, ƙasar da na rantse zan ba kakanninku.
43 A nan za ku tuna da ayyukanku da dukan abubuwa da kuka ɓata kanku da su. Za ku ji ƙyamar kanku saboda mugayen abubuwa da kuka aikata.
44 Za ku sani ni ne Ubangiji sa'ad da na yi muku haka saboda sunana, ba saboda mugayen ayyukanku ba, ya ku mutanen Isra'ila. Ni Ubangiji Allah na faɗa.”
45 Ubangiji ya yi magana da ni ya ce,
46 “Ɗan mutum, ka fuskanci wajen kudu ka ja kunnen mutanen kudu, ka kuma yi annabci gāba da kurmin ƙasar Negeb.
47 Ka ce wa kurmin Negeb, ‘Ka ji maganar Ubangiji, gama Ubangiji Allah ya ce zai kunna wuta a cikinka, za ta kuwa cinye kowane ɗanyen itace, da kowane busasshen itacen da take cikinka. Ba za a kashe harshen wutar ba. Harshen wutar zai babbake kowace fuska daga kudu zuwa arewa.