22 “Domin haka, ya Oholiba, ni, Ubangiji Allah na ce zan kuta kwartayenki su yi gāba da ke, waɗanda kika ji ƙyamarsu, kika rabu da su. Daga kowane sashi zan sa su zo su yi gāba da ke.
23 Babilawa da dukan Kaldiyawa, da Fekod, da Showa, da Kowa, da dukan Assuriyawa tare da su, wato samari masu bansha'awa. Dukansu masu mulki ne, da shugabanni, da jarumawa, da shahararru, dukansu suna kan dawakai.
24 Za su zo daga arewa su yi yaƙi da ke da karusai, da kekunan dawakai, da rundunar mutane. Za su kafa miki sansani a kowace sashi su yi yaƙi da ke da sulke, da garkuwa, da kwalkwali. Zan danƙa shari'a a hannunsu, za su kuwa shara'anta ki da irin shari'arsu.
25 Zan yi fushi da ke don su wulakanta ki. Za su datse hancinki da kunnuwanki. Waɗanda suka rage miki za a kashe su da takobi. Za su kama 'ya'yanki mata da maza, waɗanda suka rage miki kuwa, za a ƙone su da wuta.
26 Za su tsiraita ki, su kuma kwashe lu'ulu'anki.
27 Zan ƙarasa lalatarki da karuwancinki da kika kawo daga ƙasar Masar, don kada ki ƙara ɗaga idonki ki dubi Masarawa, ko ki ƙara tunawa da su.
28 “Gama ni Ubangiji Allah na ce, ‘Ga shi, zan danƙa ki a hannun waɗanda kike ƙinsu, waɗanda kika ƙi su, kika kuwa rabu da su.