10 Ubangiji Allah ya ce,“Zan sa dukiyar Masar ta ƙareTa hannun Nebukadnezzar, Sarkin Babila,
11 Shi da mutanensa,Mutane mafi bantsoro a cikin sauran al'umma,Za a kawo su don su hallakar da ƙasar.Za su zare takubansu a kan Masar,Su cika ƙasar da gawawwaki.
12 Zan busar da Kogin Nilu,Zan kuma sayar da ƙasar ga mugaye.Zan sa ƙasar ta lalaceDa dukan abin da yake cikinta,Ta hannun baƙi,Ni Ubangiji, na faɗa.”
13 Ubangiji Allah ya ce,“Zan hallakar da gumakaDa siffofi a Memfis.Ba za a ƙara samun hakimi a ƙasar Masar ba,Saboda haka zan aukar da tsoro a ƙasar Masar.
14 Zan sa Fatros ta zama kufai,Zan kunna wa Zowan wuta,Zan kuma shara'anta No.
15 Zan kwarara hasalata a kan Felusiyum,Wato kagarar Masar,Zan datse jama'ar No.
16 Zan kunna wa Masar wuta.Felusiyum za ta sha azaba mai tsanani,No kuwa za a tayar mata da hankali,Za a rurrushe garukanta.Za a tasar wa Memfis dukan yini.