14 saboda haka ba za ku ƙara cinye mutane ba, ba kuwa za ku ƙara kashe 'ya'yan al'ummarku ba. Ni Ubangiji Allah na faɗa.
15 Ba zan ƙara bari ku sha zargi wurin sauran al'umma ba, ba kuwa za ku ƙara shan kunya a gaban jama'a ba, ba kuma zan ƙara sa al'ummarku ta yi tuntuɓe ba, ni Ubangiji Allah na faɗa.”
16 Ubangiji Kuma ya yi magana da ni, ya ce,
17 “Ɗan mutum, sa'ad da mutanen Isra'ila suka zauna a ƙasar kansu, sun ƙazantar da ita ta wurin hanyoyinsu da ayyukansu. Halinsu a gare ni ya zama kamar rashin tsarkin mace a lokacin hailarta.
18 Sai na husata da su saboda jinin da suka zuba a cikin ƙasar, da kuma yadda suka ƙazantar da ƙasar da gumakansu.
19 Na warwatsa su cikin al'ummai, suka kuwa warwatsu cikin ƙasashe. Na hukunta su gwargwadon halinsu da ayyukansu.
20 Amma sa'ad da suka tafi cikin al'ummai, sai suka ɓata sunana mai tsarki a duk inda suka tafi. Sai mutane suka yi magana a kansu cewa, ‘Waɗannan jama'ar Ubangiji ne, amma dole ne su fita daga cikin ƙasarsa.’