25 Zan yayyafa muku tsabtataccen ruwa, za ku kuwa tsarkaka daga dukan ƙazantarku, da kuma daga dukan gumakanku.
26 Zan ba ku sabuwar zuciya, in sa sabon ruhu a cikinku. Zan cire zuciya mai tauri daga gare ku, sa'an nan in sa muku zuciya mai taushi.
27 Zan sa ruhuna a cikinku, in sa ku bi dokokina, ku kiyaye ka'idodina.
28 Za ku zauna cikin ƙasar da na ba kakanninku. Za ku zama mutanena, ni kuma in zama Allahnku.
29 Zan tsarkake ku daga dukan ƙazantarku. Zan kuma sa hatsi ya yi yalwa, ba zan bar yunwa ta same ku ba.
30 Zan sa 'ya'yan itatuwa da amfanin gona su yalwata, don kada ku ƙara shan kunya saboda yunwa a wurin al'ummai.
31 Sa'an nan za ku tuna da mugayen hanyoyinku da ayyukanku marasa kyau. Za ku kuwa ji ƙyamar kanku saboda muguntarku da ayyukanku na banƙyama.