29 Zan tsarkake ku daga dukan ƙazantarku. Zan kuma sa hatsi ya yi yalwa, ba zan bar yunwa ta same ku ba.
30 Zan sa 'ya'yan itatuwa da amfanin gona su yalwata, don kada ku ƙara shan kunya saboda yunwa a wurin al'ummai.
31 Sa'an nan za ku tuna da mugayen hanyoyinku da ayyukanku marasa kyau. Za ku kuwa ji ƙyamar kanku saboda muguntarku da ayyukanku na banƙyama.
32 Ni Ubangiji Allah na ce, sai ku sani, ba saboda ku ba ne zan aikata wannan. Ku kunyata, ku gigita saboda hanyoyinku, ya mutanen Isra'ila!”’
33 Ubangiji Allah ya ce, “A ranar da zan tsarkake ku daga dukan muguntarku, zan sa ku zauna cikin biranenku, ku gina rusassun wurare.
34 Ƙasar da take kufai a dā za ku kafce ta maimakon yadda take kufai a kan idon dukan masu wucewa.
35 Za su ce, ‘Wannan ƙasa wadda take kufai a dā ta zama kamar gonar Aidan, ga kuma rusassun wuraren da suka zama kufai, da rusassun birane, yanzu ana zaune a cikinsu, an kuma gina musu garu.’