4 “Sai kuma ka kwanta a hagunka, ni kuwa zan ɗora maka muguntar Isra'ilawa. Za ka ɗauki muguntarsu bisa ga yawan kwanakin da za ka kwanta a hagunka.
5 Gama na ɗora maka kwanaki bisa ga shekarun muguntarsu, wato kwana ɗari uku da tasa'in da za ka kwanta. Ta haka za ka ɗauki alhakin muguntar mutanen Isra'ila.
6 Sa'ad da ka cika waɗannan kwanaki, sai ka sāke kwantawa, kwanciya ta biyu, a damanka kwana arba'in don ka ɗauki alhakin muguntar mutanen Yahuza. Kwana ɗaya a bakin shekara guda.
7 “Za ka fuskanci Urushalima wadda aka kewaye ta da yaƙi da hannunka a zāge, sa'an nan ka yi annabci a kanta.
8 Ga shi, zan ɗaure ka da igiyoyi don kada ka juya har ka gama misalin adadin kwanakin da za a kewaye Urushalima da yaƙi.
9 “Ka kuma ɗauki alkama, da sha'ir, da wake, da waken soya, da gero, da acca, ka haɗa su a kasko ɗaya, ka yi abinci da su. Shi ne za ka ci a kwanakin na ɗari uku da tasa'in da za ka kwanta.
10 Za a auna maka abincin da za ka ci, kamar nauyin shekel ashirin ne a yini. Za ka ci shi a ƙayyadadden lokaci kowace rana.