9 “Ka kuma ɗauki alkama, da sha'ir, da wake, da waken soya, da gero, da acca, ka haɗa su a kasko ɗaya, ka yi abinci da su. Shi ne za ka ci a kwanakin na ɗari uku da tasa'in da za ka kwanta.
10 Za a auna maka abincin da za ka ci, kamar nauyin shekel ashirin ne a yini. Za ka ci shi a ƙayyadadden lokaci kowace rana.
11 Za a kuma auna maka ruwan da za ka sha, misalin kwalaba biyu ga yini. Za ka sha ruwan a ƙayyadadden lokaci kowace rana.
12 Za ka yi waina kamar ta sha'ir, ka ci. Za ka toya ta da najasa a idon jama'a.”
13 Ubangiji ya ce, “Haka jama'ar Isra'ila za su ci ƙazantaccen abincinsu a cikin sauran al'umma inda za a kai su bautar talala.”
14 Sai na ce, “Ya Ubangiji Allah, ban taɓa ƙazantar da kaina ba. Tun daga ƙuruciyata har zuwa yau, ban taɓa cin mushe ba, ko abin da namomin jeji suka kashe. Ƙazantaccen nama bai taɓa shiga bakina ba.”
15 Sa'an nan ya ce mini, “To, zan bar ka ka mori taroson shanu maimakon najasa, don ka dafa abincinka.”