2 A cikin wahayi, sai Allah ya kai ni ƙasar Isra'ila, ya zaunar da ni a kan wani dutse mai tsayi ƙwarai, inda na ga wani fasali kamar birni daura da ni.
3 Sa'ad da ya kai ni can sai ga wani mutum, kamanninsa sai ka ce tagulla, yana riƙe da igiyar rama da wani irin ƙara na awo a hannunsa, yana tsaye a bakin ƙofa.
4 Sai mutumin nan ya ce mini, “Ɗan mutum ka duba da idonka, ka ji da kunnuwanka, ka kuma mai da hankali ga dukan abin da zan nuna maka, gama saboda haka aka kawo ka nan. Sai ka sanar wa jama'ar Isra'ila abin da ka gani duka.”
5 Abin da na gani Haikali ne. Akwai katanga kewaye da filin Haikalin. Tsawon karan awon kuma da yake a hannun mutumin kamu shida ne. Sai ya auna faɗin katangar ya sami kamu shida, tsayinta kuma kamu shida.
6 Ya tafi kuma wajen ƙofar gabas ya hau matakanta, ya auna dokin ƙofar, faɗinta kamu shida ne.
7 Tsawon ɗakin 'yan tsaro kamu shida ne, faɗinsa kuma kamu shida. Kamu biyar ne yake tsakanin ɗaki da ɗaki. Dokin ƙofa kuma da yake kusa da shirayin bakin ƙofar Haikali kamu shida ne.
8 Ya kuma auna shirayin bakin ƙofar da take fuskantar Haikali, kamu shida.