23 Fili na ciki yana da ƙofa daura da ƙofar arewa da ta gabas. Ya auna daga ƙofa zuwa ƙofa kamu ɗari.
24 Ya kuma kai ni wajen kudu, sai kuma ga wata ƙofa. Ya auna ginshiƙanta da shirayinta. Girmansu ɗaya ne, kamar na sauran.
25 Akwai tagogi kewaye da ƙofar, da shirayinta kamar na sauran. Tsayinta kamu hamsin ne, faɗinta kuwa kamu ashirin da biyar.
26 Tana da matakai bakwai. Shirayinta yana daga can ciki. An zana siffar itatuwan dabino a ginshiƙanta, ɗaya a kowane gefe.
27 Akwai wata ƙofa a kudancin fili na can ciki. Ya auna daga ƙofa zuwa ƙofa kamu ɗari.
28 Ya kuma kai ni fili na can ciki, wajen ƙofar kudu, sai ya auna ƙofar, girmanta daidai yake da na sauran.
29 Haka kuma ɗakunanta na 'yan tsaro, da ginshiƙanta, da shirayinta, girmansu ɗaya yake da na sauran. Tana da tagogi kewaye da ita da shirayinta. Tsayinta kamu hamsin ne, faɗinta kamu ashirin da biyar ni.