46 Ɗakin da yake fuskantar arewa na firistoci ne waɗanda suke lura da bagade. Waɗannan su ne zuriyar Zadok waɗanda su kaɗai ne daga cikin Lawiyawa da suke da iznin kusatar Ubangiji don su yi masa hidima.”
47 Ya auna filin, tsawonsa kamu ɗari ne, faɗinsa kuma kamu ɗari, wato murabba'i ke nan. Bagade kuma yana a gaban Haikalin.
48 Ya kuma kai ni a shirayin Haikalin. Ya auna ginshiƙan shirayin, kamu biyar ne a kowane gefe. Faɗin ƙofar kuwa kamu uku ne a kowane gefe.
49 Tsawon shirayin kamu ashirin ne, faɗinsa kuwa kamu goma sha ɗaya. Akwai matakan hawa, akwai kuma ginshiƙai a kowane gefe.