7 Tsawon ɗakin 'yan tsaro kamu shida ne, faɗinsa kuma kamu shida. Kamu biyar ne yake tsakanin ɗaki da ɗaki. Dokin ƙofa kuma da yake kusa da shirayin bakin ƙofar Haikali kamu shida ne.
8 Ya kuma auna shirayin bakin ƙofar da take fuskantar Haikali, kamu shida.
9 Sa'an nan ya auna shirayin bakin ƙofar kamu takwas ne. Sai kuma ya auna ginshiƙan shirayin kamu biyu ne. Shirayin ƙofar yana fuskantar ciki.
10 Akwai ɗakuna uku na 'yan tsaro a kowane gefe na ƙofar gabas, girmansu iri ɗaya ne. Ginshiƙansu kuma girmansu ɗaya ne.
11 Ya kuma auna fāɗin bakin ƙofar, kamu goma ne, tsayin ƙofar kuwa kamu goma sha uku ne.
12 Akwai, 'yar katanga a gaban ɗakunan 'yan tsaron, faɗinta kamu ɗaya ne a kowane gefe. Girman ɗakunan 'yan tsaron kuwa kamu shida ne a kowane gefe.
13 Daga bayan rufin ɗaya ɗakin 'yan tsaro zuwa bayan ɗayan rufin ya auna filin ya sami kamu ashirin da biyar.