Ez 48:15-21 HAU

15 “Ragowar yankin mai faɗin kamu dubu biyar [5,000], da tsawon kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000], zai zama hurumin birnin, inda za a yi gidaje da wurin kiwo. Birnin zai kasance a tsakiyar yankin.

16 Ga yadda girman birnin zai kasance, a wajen arewa kamu dubu huɗu da ɗari biyar [4,500], a wajen kudu kuwa kamu dubu huɗu da ɗari biyar [4,500], a wajen gabas kamu dubu huɗu da ɗari biyar [4,500], a wajen yamma kuma kamu dubu huɗu da ɗari biyar [4,500].

17 Birnin zai kasance da hurumi a kewaye da shi. A wajen gabas kamu metan da hamsin, a wajen yamma kamu metan da hamsin, a wajen kudu kamu metan da hamsin, a wajen arewa kuma kamu metan da hamsin.

18 Ragowar tsawon yankin da yake gab da tsattsarkan yankin, zai zama kamu dubu goma [10,000] a wajen gabas, a wajen yamma kamu dubu goma [10,000]. Amfanin da yankin zai bayar, zai zama abincin ma'aikatan birnin.

19 Ma'aikatan birnin za su samu daga dukan kabilan Isra'ila, za su noma yankin.

20 Dukan yankin da za ku keɓe zai zama murabba'i mai kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000], wato tsattsarkan yankin tare da hurumin birnin.

21 “Ragowar kowane gefe na tsattsarkan yankin da hurumin birnin, zai zama na sarki. Tun daga kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000] na tsattsarkan yankin, zuwa iyakar da take wajen gabas, daga kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000] kuma zuwa iyakar wajen yamma, hannun riga da yankunan kabilan zai zama na sarki. Tsattsarkan yankin da wuri mai tsarki na Haikali za su kasance a tsakiyarsa.