8 Sa'ad da suke karkashewar, aka bar ni, ni kaɗai, sai na faɗi rubda ciki, na yi kuka, na ce, “Ya Ubangiji Allah za ka hallaka dukan sauran Isra'ilawa saboda zafin fushinka a kan Urushalima?”
9 Sa'an nan ya ce mini, “Zunubin mutanen Isra'ila da Yahuza ya kasaita ƙwarai. Ƙasar tana cike da jini, birnin kuma yana cike da rashin imani, gama sun ce, ‘Ubangiji ya rabu da ƙasar, ba ya ganinmu.’
10 Ni kam, idona ba zai yafe ba, ba kuwa zan ji tausayi ba, amma zan sāka musu bisa ga ayyukansu.”
11 Sai ga mutumin da yake saye da rigar lilin, wanda kuma yake rataye da gafaka, ya komo da jawabi cewa, “Na aikata yadda ka umarci ni.”