25 Wannan ya yi nesa da kai, da ka aikata irin haka, wato da za ka aza mai adalci daidai yake da mugu! Wannan ya yi nesa da kai! Mahukuncin dukan duniya ba zai yi adalci ba?”
26 Sai Ubangiji ya ce, “In na sami adalai hamsin a cikin birnin Saduma, zan yafe wa dukan wurin sabili da su.”
27 Ibrahim ya amsa ya ce, “Ga shi, na jawo wa kaina in yi magana da Ubangiji, ni da nake ba kome ba ne, amma turɓaya ne da toka.
28 Da a ce za a rasa biyar daga cikin adalai hamsin ɗin, za ka hallaka birnin duka saboda rashin biyar ɗin?”Sai ya ce, “Ba zan hallaka shi ba in na sami arba'in da biyar a wurin.”
29 Ya kuma sāke yin masa magana, ya ce, “Da a ce za a sami arba'in a wurin fa?”Ya amsa ya ce, “Sabili da arba'in ɗin ba zan yi ba.”
30 Sai ya ce, “Kada dai Ubangiji ya husata, zan yi magana. Da a ce za a sami talatin a wurin fa?”Ya amsa, “Ba zan yi ba, in na sami talatin a wurin.”
31 Ya ce, “Ga shi, na jawo wa kaina in yi magana da Ubangiji. Da a ce za a sami ashirin a wurin fa?”Ya amsa ya ce, “Sabili da ashirin ɗin ba zan hallaka shi ba.”