25 Sa'ad da mutumin ya ga bai rinjayi Yakubu ba sai ya taɓa kwarin kwatangwalonsa, sai gaɓar kwatangwalon Yakubu ta gulle a lokacin da yake kokawa da shi.
26 Sa'an nan sai mutumin ya ce, “Ka bar ni in tafi, gama gari na wayewa.”Amma Yakubu ya ce, “Ba zan bar ka ka tafi ba, sai ka sa mini albarka.”
27 Sai ya ce masa, “Yaya sunanka?”Ya ce, “Yakubu.”
28 Sai ya ce, “Ba za a ƙara kiranka da suna Yakubu ba, amma za a kira ka Isra'ila, gama ka yi kokawa da Allah da mutane, ka kuwa yi rinjaye.”
29 Sa'an nan Yakubu ya tambaye shi, “Ina roƙonka, faɗa mini sunanka.”Amma ya ce, “Don me kake tambayar sunana?” A nan mutumin ya sa masa albarka.
30 Saboda haka Yakubu ya sa wa wurin suna Feniyel, yana cewa, “Gama na ga Allah fuska da fuska, duk da haka ban mutu ba.”
31 Rana ta yi sama a sa'ad da Yakubu ya wuce Feniyel domin yana ɗingishi saboda kwatangwalonsa.