5 Gumakansu dodon gona suke, acikin gonar kabewa,Ba su iya yin magana,Ɗaukarsu ake yi domin ba su iyatafiya!Kada ku ji tsoronsu.Gama ba su da ikon aikata muguntako alheri.”
6 Ya Ubangiji, ba wani kamarka,Kai mai girma ne,Sunanka kuma yana da girma daiko.
7 Wane ne ba zai ji tsoronka ba, yaSarkin dukan al'ummai?Ka isa a ji tsoronka,Gama babu kamarka a cikin dukanmasu hikima na al'ummai,Da kuma cikin dukan mulkokinsu,Ba wani kamarka.
8 Dukansu dakikai ne wawaye,Koyarwar gumaka ba wani abu bane, itace ne kawai!
9 An kawo fallayen azurfa dagaTarshish,Da zinariya kuma daga Ufaz,Aikin gwanaye da maƙeranzinariya.Tufafinsu na mulufi ne da shunayya,duka aikin gwanaye.
10 Amma Ubangiji shi ne Allah nagaskiya,Shi Allah mai rai ne,Shi Sarki ne madawwami.Saboda hasalarsa duniya ta girgiza,Al'ummai ba za su iya jurewa dafushinsa ba.
11 Haka za ku faɗa musu, “Gumakan da ba su yi sammai da duniya ba, za su lalace a duniya da a ƙarƙashin sammai.”