10 Sun koma a kan laifofin kakanninsu, waɗanda suka ƙi jin maganata, suka bi gumakansu don su bauta musu, jama'ar Isra'ila da na Yahuza sun ta da alkawarina wanda na yi da kakanninsu.
11 Saboda haka ni Ubangiji na ce, ‘Ga shi, ina kawo musu masifa wadda ba za su iya tsere mata ba, ko da za su yi kuka gare ni ba zan ji su ba.
12 Sa'an nan biranen Yahuza da mazaunan Urushalima za su tafi, su yi kuka ga gumaka waɗanda suka ƙona musu turare, amma ba za su iya cetonsu a lokacin wahalarsu ba.
13 Gama yawan gumakansu sun kai yawan biranensu. Yawan bagadan da suke da su kuma sun kai yawan titunan Urushalima, abin kunya, bagadan ƙona wa Ba'al turare ne.’
14 Don haka kada ka yi wa waɗannan mutane addu'a. Kada ka yi kuka ko addu'a dominsu, gama ba zan kasa kunne gare su ba, ko da sun yi kirana a lokacin wahalarsu.”
15 Ubangiji ya ce, “Wane iko ƙaunatacciyata take da shi cikin Haikalina, da ya ke ta aikata mugayen ayyuka? Ko alkawarai da naman hadayu za su iya kawar miki da ƙaddararki, har da za ki yi taƙama?
16 Dā na kira ki itacen zaitun mai duhuwa, kyakkyawa, mai kyawawan 'ya'ya, amma da ƙugin babbar iska za a cinna miki wuta, za ta kuwa cinye rassanki.”