4 Sai yaushe ƙasar za ta dainamakoki,Ciyawar kowace saura kuma ta dainayin yaushi?Saboda muguntar mazaunan ƙasarne dabbobi da tsuntsaye sukaƙare,Domin mutanen suna cewa, “Ba zaiga ƙarshenmu ba.”
5 Ubangiji ya ce,“Idan kai da mutane kun yi tserenƙafa sun gajiyar da kai,Yaya za ka iya gāsa da dawakai?Idan ka fāɗi a lafiyayyiyar ƙasa,Ƙaƙa za ka yi a kurmin Urdun?
6 Gama har da 'yan'uwanka da gidanmahaifinka,Sun ci amanarka,Suna binka da kuka,Kada ka gaskata su,Ko da yake suna faɗa makamaganganu masu daɗi.”
7 Ubangiji ya ce,“Na bar jama'ata.Na rabu da gādona,Na ba da wanda raina yake ƙauna ahannun maƙiyansa.
8 Abin gādona ya zama mini kamarzaki a cikin kurmi,Ya ta da murya gāba da ni,Domin haka na ƙi shi.
9 Ashe, abin gadon nan nawa ya zamadabbare-dabbaren tsuntsun nan nemai cin nama?Tsuntsaye masu cin nama sun kewayeshi?Tafi, ka tattaro namomin jeji,Ka kawo su su ci.
10 Makiyaya da yawa sun lalatar dagonar inabina.Sun tattake nawa rabo,Sun mai da nawa kyakkyawan rabokufai da hamada.