17 Gama ina ganin dukan ayyukansu, ba a ɓoye suke a gare ni ba, muguntarsu kuma ba a ɓoye take a gare ni ba.
18 Zan riɓaɓɓanya sakayyar da zan yi musu saboda muguntarsu da zunubinsu, domin sun ƙazantar da ƙasata da ƙazantattun gumakansu marasa rai, abin gādona kuma sun cika shi da abubuwansu na banƙyama.”
19 “Ya Ubangiji, ƙarfina da kagarata,Mafakata a ranar wahala,A gare ka al'ummai za su zo,Daga ƙurewar duniya, su ce,‘Kakanninmu ba su gāji kome ba, saiƙarya,Da abubuwan banza marasaamfani.’
20 Mutum zai iya yi wa kansa alloli?Ai, waɗannan ba alloli ba ne!”
21 Ubangiji ya ce,“Saboda haka, ga shi, zan sa su sani,Sau ɗayan nan kaɗai zan sa su su sanikona da ƙarfina,Za su kuma sani sunana Ubangijine.”