17 Ya Isra'ila, kai ne ka jawo wa kankawannan,Da ka rabu da Ubangiji Allahnka,Sa'ad da ya bishe ka a hanya.
18 Wace riba ka samu, har da ka tafiMasar,Don ka sha ruwan Kogin Nilu?Wace riba ka samu, har da ka tafiAssuriya,Don ka sha ruwan KoginYufiretis?
19 Muguntarka za ta hore ka,Riddarka kuma za ta hukunta ka.Sa'an nan za ka sani, ka kumagane,Ashe, mugun abu ne, mai ɗaci, a garekaKa rabu da Ubangiji Allahnka,Ba ka tsorona a zuciyarka.Ni Ubangiji, Allah Mai Runduna nafaɗa.”
20 “Ya Isra'ila, tun da daɗewa, ka ƙiyardaUbangiji ya mallake ka,Ka ƙi yin biyayya da ni,Ka kuwa ce, ‘Ba zan yi bauta ba.’Amma ka yi karuwanci a kankowane tudu,Da kowane ɗanyen itace.
21 Na dasa ka kamar zaɓaɓɓiyarkurangar inabi, zaɓaɓɓen iri mafikyau.Ta yaya ka lalace haka ka zamarassan kurangar inabi ta jeji,Waɗanda ba zan yarda da su ba?
22 Ko da za ka yi wanka da sabulunsalo,Ka yi amfani da sabulu mai yawa,Duk da haka zan ga tabbanzunubanka.Ni Ubangiji Allah na faɗa.
23 Ƙaƙa za ka ce ba ka ƙazantar dakanka ba,Ba ka taɓa bin gunkin nan Ba'al ba?Ka duba hanyarka ta zuwa cikinkwari, ka san abin da ka yi.Kana kama da taguwa, mai yawonneman barbara.