14 Kaiton wanda ya ce,“Zan gina wa kaina babban gidaDa waɗansu irin benayemusamman.”Ya yi masa tagogi,Ya manna masa itacen al'ul,Sa'an nan ya yi masa jan shafe.
15 Kana tsammani kai sarki ne,Da yake ƙasarka ta itacen al'ulce?Amma ubanka ya ci, ya sha,Ya yi gaskiya, ya aikata adalci,Ya kuwa zauna lafiya.
16 Ya biya wa matalauta da masubukata hakkinsu,Ya kuwa yi kyau.Abin da ake nufi da sanina ke nan,In ji Ubangiji.
17 Amma ka sa idonka da zuciyarka gaƙazamar riba,Da zubar da jinin marar laifi,Da yin zalunci da danniya.
18 Domin haka ga abin da Ubangiji ya ce a kan Yehoyakim ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza,“Ba za su yi makoki dominsa ba, kosu ce,‘Wayyo ɗan'uwanmu!’ ko, ‘Wayyo'yar'uwarmu!’Ba za su yi makoki dominsa ba, suce,‘Wayyo ubangidanmu!’ ko ‘Wayyo mai martaba!’
19 Za a binne shi kamar jaki,Za a ja shi a yar a bayan ƙofofinUrushalima.”
20 Ku haura zuwa Lebanon, ku yikuka,Ku ta da muryarku cikin Bashan,Ku yi kuka daga Abarim,Gama an hallakar da dukanƙaunatattunku.