13 “A cikin annabawan Samariya,Na ga abu marar kyan gani.Da sunan Ba'al suke yin annabci,Suna ɓad da jama'ata Isra'ila
14 Amma cikin annabawa naUrushalima,Na ga abin banƙyama.Suna yin zina, suna ƙarya,Suna ƙarfafa hannuwan masu aikatamugunta,Saboda haka ba wanda ya juya gabarin muguntarsa,Dukansu suna kama da Saduma,Mazaunanta kuwa kamarGwamrata.”
15 Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Runduna ya ce a kan annabawa,“Ga shi, zan ciyar da su da abincimai ɗaci,In shayar da su da ruwan dafi.Daga wurin annabawan UrushalimaRashin tsoron Allah ya fito yamamaye dukan ƙasar.”
16 Ubangiji Mai Runduna ya ce wamazaunan Urushalima,“Kada ku kasa kunne ga maganarannabawa,Gama sukan cika kunnuwanku daƙarairayi.Suna faɗar ganin damarsu,Ba faɗar Ubangiji ba.
17 Suna ta faɗa wa waɗanda suke rainamaganar Ubangiji cewa,‘Za ku zauna lafiya!’Ga kowane mai bin nufin tattaurarzuciyarsa,‘Ba masifar da za ta same ka.’ ”
18 Irmiya ya ce, “Gama wane ne a cikin annabawan nan ya taɓa neman shawarar Ubangiji don ya fahimci maganarsa, ko kuwa wane ne ya taɓa kasa kunne don ya ji maganarsa?
19 Ga shi, hadirin hasalar Ubangiji yataso,Kamar iskar guguwa,Zai tashi a bisa kan mugaye.