21 Ubangiji ya ce,“Ni ban aiki waɗannan annabawaba,Duk da haka sun tafi,Ban kuwa yi musu magana ba,Amma sun yi annabci.
22 Amma da a ce sun tsaya cikinshawarata,Da sun yi shelar maganata gajama'ata,Da sun juyar da su daga muguwarhanyarsu,Da mugayen ayyukansu.
23 “Ni Allah na kusa ne kaɗai,Banda na nesa?” In ji Ubangiji.
24 “Mutum ya iya ɓoye kansa a wanilunguInda ba zan iya ganinsa ba?” In jiUbangiji.“Ashe, ban cika sammai da duniyaba?
25 Na ji abin da annabawan nan suka ce, su da suke annabcin ƙarya da sunana. Suna cewa, ‘Na yi mafarki!’
26 Har yaushe ƙarya za ta fita daga zuciyar annabawan nan masu annabcin ƙarya, waɗanda suke annabcin ruɗin da yake a zuciyarsu?
27 Suna zaton za su sa mutanena su manta da sunana ta wurin mafarkansu da suke faɗa wa junansu, kamar yadda kakanninsu suka manta da sunana saboda Ba'al.