14 Kada ka kasa kunne ga maganar annabawan da suke ce maka, ‘Ba za ku bauta wa Sarkin Babila ba.’ Annabcin ƙarya suke yi muku.
15 Gama Ubangiji ya ce shi bai aike su ba, annabcin ƙarya suke yi muku da sunansa, don ya kore ku, ku halaka, ku da annabawan da suke yi muku annabci.”
16 Sa'an nan na faɗa wa firistoci da jama'a cewa, “In ji Ubangiji, kada ku kasa kunne ga abin da annabawanku suke muku annabci cewa, ‘Ba da daɗewa ba za a komo da kayan Haikalin Ubangiji daga Babila.’ Ƙarya ce suke yi muku.
17 Kada ku ji su, amma ku bauta wa Sarkin Babila don ku rayu! Don me birnin nan zai zama kufai?
18 Idan su annabawa ne, idan kuwa Ubangiji yana magana da su, to, bari su roƙi Ubangiji Mai Runduna kada a tafi Babila da kayayyakin da suka ragu a Haikalin Ubangiji, da a fādar Sarkin Yahuza, da a Urushalima.
19 Gama Ubangiji Mai Runduna ya faɗi zancen ginshiƙai, da babbar kwatarniya, da dakalai, da sauran kayayyaki da aka bar su a birnin nan,
20 wato waɗanda Nebukadnezzar, Sarkin Babila bai kwashe ba a lokacin da ya tafi da Yekoniya ɗan Yehoyakim, Sarkin Yahuza, da dukan dattawan Yahuza da na Urushalima zuwa bauta a Babila.