17 Haka Ubangiji Mai Runduna ya ce, ‘Ga shi, zan aiko musu da takobi, da yunwa, da masifa, zan maishe su kamar ruɓaɓɓen ɓaure waɗanda suka lalace ƙwarai, har ba su ciwuwa.
18 Zan fafare su da takobi, da yunwa, da masifa. Zan maishe su abin ƙyama ga dukan mulkokin duniya. Za su zama abin la'ana, da abin razana, da abin raini, da abin zargi, ga dukan al'ummai, inda na kora su.
19 Domin ba su ji maganata wadda ni Ubangiji na faɗa ba, na yi ta aika muku da ita ta wurin bayina annabawa, amma kuka ƙi, ni Ubangiji na faɗa.
20 Ku ji maganar Ubangiji, dukanku da aka kai ku zaman talala waɗanda na kora daga cikin Urushalima zuwa Babila.’
21 “Haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila ya ce a kan Ahab ɗan Kolaya, da Zadakiya ɗan Ma'aseya, waɗanda suke yi muku annabcin ƙarya da sunana. ‘Ga shi, zan bashe su a hannun Nebukadnezzar, Sarkin Babila, zai kashe su a kan idonku.
22 Saboda su duka waɗanda aka kai bautar talala daga Yahuza zuwa Babila, za su mori kalman nan suna yin la'ana cewa, “Ubangiji ya maishe ka kamar Zadakiya da Ahab, waɗanda Sarkin Babila ya gasa da wuta!”
23 Gama sun yi wauta a Isra'ila, sun yi zina da matan maƙwabtansu, sun yi ƙarya da sunana, ni kuwa ban umarce su ba. Ni na sani, ni ne kuma shaida, ni Ubangiji na faɗa.