23 Gama sun yi wauta a Isra'ila, sun yi zina da matan maƙwabtansu, sun yi ƙarya da sunana, ni kuwa ban umarce su ba. Ni na sani, ni ne kuma shaida, ni Ubangiji na faɗa.
24 “Zancen Shemaiya mutumin Nehelam,
25 haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila ya faɗa. Ga shi, ka aika da wasiƙu da sunanka zuwa ga dukan jama'ar da suke a Urushalima, da zuwa ga Zafaniya ɗan Ma'aseya, firist, da kuma ga dukan firistoci, cewa
26 Ubangiji ya naɗa ka firist a madadin Yehoyada firist, ka lura da Haikalin Ubangiji, ka sa kowane mahaukacin da zai yi annabci a turu, ka sa masa ƙangi.
27 To, me ya sa ba ka tsauta wa Irmiya, mutumin Anatot, wanda yake yin maka annabci ba?
28 Gama ya aiko mana a Babila, cewa za mu daɗe a zaman talala, mu gina wa kanmu gidaje, mu zauna a ciki, mu dasa gonaki mu ci amfaninsu.”
29 Sai Zafaniya firist, ya karanta wasiƙan nan a gaban annabi Irmiya.