15 Don me kuke kuka a kanrauninku?Ciwonku ba zai warke ba.Saboda laifofinku masu girma ne,Domin zunubanku da yawa suke,Shi ya sa na yi muku waɗannanabubuwa.
16 Domin haka dukan waɗanda sukacinye ku, za a cinye su,Dukan maƙiyanku, kowane ɗayansuzai tafi bauta,Waɗanda suka washe ku, za a washesu.Dukan waɗanda suka kwashe kuganima, su ma za a kwashe suganima.
17 Zan mayar muku da lafiyarku,Zan kuma warkar da raunukanku,Ko da yake maƙiyanku sunakiranku yasassu,Suna cewa, ‘Ai, Sihiyona ce, bawanda ya kula da ita.’Ni Ubangiji na faɗa.”
18 Ubangiji ya ce,“Ga shi, zan komar wa alfarwarYakubu arzikinta,Zan kuma nuna wa wuraren zamansajinƙai,Za a sāke gina birnin a kufansa,Fādar kuma za ta kasance a indatake a dā.
19 Daga cikinsu za a ji waƙoƙin godiya.Da muryoyin masu murna.Zai riɓaɓɓanya su, ba za su zamakaɗan ba,Zan kuwa ɗaukaka su, ba za aƙasƙantar da su ba.
20 'Ya'yansu za su zama kamar dā,Jama'arsu kuma za su kahu agabana,Zan hukunta dukan waɗanda sukazalunce su.
21 Sarkinsu zai zama ɗaya dagacikinsu,Mai mulkinsu kuma zai fito dagacikinsu.Zan kawo shi kusa, zai kuwa kusaceni,Gama wane ne zai yi ƙarfin hali yakusace ni? Ni Ubangiji na faɗa.