19 wato manyan fādawan Yahuza, da na Urushalima, da 'yan majalisa, da firistoci da dukan jama'ar ƙasa, waɗanda suka bi ta tsakanin rababben ɗan maraƙin,
20 zan bashe su a hannun abokan gabansu waɗanda suke neman ransu. Gawawwakinsu za su zama abincin tsuntsaye da namomin jeji.
21 Zadakiya, Sarkin Yahuza kuwa, da sarakunansa, zan bashe su a hannun abokan gābansu waɗanda suke neman ransu, wato sojojin Sarkin Babila, waɗanda suka tashi suka bar ku.
22 Ni Ubangiji zan umarce su su komo zuwa wannan birni don su yi yaƙi da shi, su ci shi, su ƙone shi da wuta. Zan sa biranen Yahuza su zama kufai, ba masu zama a ciki.”