4 Sai Irmiya ya kirawo Baruk ɗan Neriya. Baruk kuwa ya rubuta maganar da Irmiya ya faɗa masa a takarda, wato dukan maganar da Ubangiji ya faɗa wa Irmiya.
5 Sai Irmiya ya umarci Baruk, ya ce, “An hana ni zuwa Haikali,
6 saboda haka kai za ka tafi. A ranar azumi za ka karanta wa mutane maganar Ubangiji, wadda take a takardar da ka rubuta ta wurin shibtar da na yi maka. Ka karanta ta a cikin Haikali, a gaban mutanen Yahuza waɗanda suka fito daga biranensu.
7 Mai yiwuwa ne za su roƙi Ubangiji, su tuba, su bar mugayen ayyukansu, gama Ubangiji yana fushi ƙwarai, Ubangiji ya hurta hasala a kan wannan jama'a.”
8 Sai Baruk ɗan Neriya ya yi dukan abin da annabi Irmiya ya umarce shi. Ya karanta takardan nan ta maganar Ubangiji a Haikalin Ubangiji.
9 A watan tara a shekara ta biyar ta sarautar Yehoyakim ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza, sai dukan jama'ar Urushalima da dukan jama'ar da suka zo Urushalima daga biranen Yahuza suka yi shela a yi azumi a gaban Ubangiji.
10 Sai Baruk ya karanta maganar Irmiya wadda take a takardar, kowa yana ji, a cikin Haikali a ɗakin Gemariya ɗan Shafan, magatakarda. Ɗakinsa yana a shirayi na bisa a hanyar shiga Sabuwar Ƙofa ta Haikalin Ubangiji.