19 Sarki Zadakiya ya ce wa Irmiya, “Ina jin tsoron Yahudawa waɗanda suka gudu zuwa wurin Kaldiyawa. Kila a bashe ni a hannunsu, su ci mutuncina.”
20 Irmiya kuwa ya ce masa, “Ba za a bashe ka gare su ba. Kai dai ka yi biyayya da maganar Ubangiji wadda nake faɗa maka yanzu. Yin haka zai fi maka amfani, za ka tsira.
21 Amma idan ka ƙi miƙa wuya, to, ga abin da Ubangiji ya nuna mini a wahayi.
22 Ga shi, dukan matan da suka ragu a gidan Sarkin Yahuza, za a kai su wurin sarakunan Sarkin Babila, suna cewa,‘Aminanka sun ruɗe ka,Sun rinjaye ka.Yanzu sun ga ƙafafunka sun nutsecikin laka,Sai suka rabu da kai.’
23 “Dukan matanka da 'ya'yanka za a kai su wurin Kaldiyawa, kai kanka kuma ba za ka tsere musu ba, amma Sarkin Babila zai kama ka, birnin kuma za a ƙone shi da wuta.”
24 Sai Zadakiya ya ce wa Irmiya, “Kada ka bar wani ya san wannan magana, kai kuwa ba za a kashe ka ba.
25 Idan sarakuna suka ji, wai na yi magana da kai, in suka zo wurinka, suka ce, ‘Ka faɗa mana abin da ka faɗa wa sarki da abin da sarki ya faɗa maka, kada ka ɓoye mana kome mu kuwa ba za mu kashe ka ba.’