1 A watan goma a na shekara ta tara ta sarautar sarki Zadikiya, Sarkin Yahuza, sai Nebukadnezzar Sarkin Babila, da dukan sojojinsa suka zo, suka kewaye Urushalima da yaƙi.
2 A rana ta tara ga watan huɗu, a shekara ta goma sha ɗaya ta sarautar Zadakiya, sai aka huda garun birnin.
3 Sa'an nan da aka ci Urushalima, sai dukan sarakunan Sarkin Babila suka shiga, suka zauna a Ƙofar Tsakiya. Sarakuna, su ne Nergal-sharezer, da Samgar-nebo, da Sarsekim, wato Rabsaris, da Nergal-sharezer, wato Rabmag, da dukan sauran shugabannin Sarkin Babila.
4 Sa'ad da Zadakiya, Sarkin Yahuza, da dukan sojoji suka gan su, sai suka gudu, suka fita daga birnin da dare, ta hanyar gonar sarki a ƙofar da take a tsakanin garu biyu. Suka nufi zuwa wajen Araba.
5 Amma sojojin Kaldiyawa suka bi su, suka ci wa Zadakiya a filayen Yariko. Suka kama shi, suka kawo shi gaban Sarkin Babila a Ribla a ƙasar Hamat, a can Nebukadnezzar ya yanka masa hukunci.
6 Sarkin Babila ya kashe 'ya'yan Zadakiya, maza, a Ribla a kan idon Zadakiya. Ya kashe dukan shugabannin Yahuza.