6 Sarkin Babila ya kashe 'ya'yan Zadakiya, maza, a Ribla a kan idon Zadakiya. Ya kashe dukan shugabannin Yahuza.
7 Ya kuma ƙwaƙule idanun Zadakiya, ya buga masa ƙuƙumi, ya kai shi Babila.
8 Sai Kaldiyawa suka ƙone gidan sarki, da gidajen jama'a. Suka kuma rushe garun Urushalima.
9 Sa'an nan Nebuzaradan shugaban matsara ya kwashi sauran mutane da suka ragu a birnin zuwa babila, wato mutanen da suka gudu zuwa wurinsa.
10 Amma ya bar matalauta waɗanda ba su da kome a ƙasar. Ya ba su gonakin inabi da waɗansu gonaki a ran nan.
11 Sai Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya yi wa Nebuzaradan shugaban matsara umarni a kan Irmiya ya ce,
12 “Ka ɗauke shi ka lura da shi da kyau, kada ka yi masa wani mugun abu, amma ka yi masa dukan abin da yake so.”