8 Sai Kaldiyawa suka ƙone gidan sarki, da gidajen jama'a. Suka kuma rushe garun Urushalima.
9 Sa'an nan Nebuzaradan shugaban matsara ya kwashi sauran mutane da suka ragu a birnin zuwa babila, wato mutanen da suka gudu zuwa wurinsa.
10 Amma ya bar matalauta waɗanda ba su da kome a ƙasar. Ya ba su gonakin inabi da waɗansu gonaki a ran nan.
11 Sai Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya yi wa Nebuzaradan shugaban matsara umarni a kan Irmiya ya ce,
12 “Ka ɗauke shi ka lura da shi da kyau, kada ka yi masa wani mugun abu, amma ka yi masa dukan abin da yake so.”
13 Sai Nebuzaradan shugaban matsara, da Nebushazban, wato Rabsaris, da Nergal-sharezer, wato Rabmag, da dukan shugabannin Sarkin Babila,
14 suka aika aka kawo Irmiya daga gidan waƙafi, suka ba da Irmiya amana ga Gedaliya, ɗan Ahikam ɗan Shafan, don ya kai shi gida. Da haka Irmiya ya zauna tare da mutane.