5 Sa'an nan suka ce wa Irmiya, “Ubangiji mai gaskiya, mai aminci ya zama shaida a tsakaninmu, idan ba mu yi duk yadda Ubangiji Allahnka ya aiko ka gare mu ba.
6 Ko nagari ne ko mugu ne, za mu yi biyayya da muryar Ubangiji Allahnmu wanda muka aike ka wurinsa, gama zai zama alheri a gare mu idan mun yi biyayya da muryar Ubangiji Allahnmu.”
7 Bayan kwana goma sai Ubangiji ya yi magana da Irmiya.
8 Sai Irmiya ya kira Yohenan ɗan Kareya da dukan shugabannin sojoji waɗanda suke tare da shi, da dukan jama'a tun daga ƙarami har zuwa babba.
9 Ya ce musu, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra'ila, wanda kuka aike ni da koke-kokenku wurinsa ya ce,
10 ‘Idan za ku zauna a ƙasan nan, to, zan gina ku, ba zan rushe ku ba. Zan dasa ku, ba zan tumɓuke ku ba, gama zan janye masifar da na aukar muku.
11 Kada ku ji tsoron Sarkin Babila, shi wanda kuke jin tsoronsa. Kada ku ji tsoronsa,’ in ji Ubangiji, ‘gama ina tare da ku, zan cece ku, in kuɓutar da ku daga hannunsa.