24 Za a kunyatar da mutanen Masar,An bashe su a hannun mutanenarewa.”
25 Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ya ce, “Ga shi, zan hukunta Amon na No, da Fir'auna, da Masar, tare da allolinta, da sarakunanta, wato Fir'auna, tare da waɗanda suke dogara gare shi.
26 Zan bashe su a hannun waɗanda suke neman ransu, wato a hannun Nebukadnezzar, Sarkin Babila, da shugabanninsa. Daga baya kuma mutane za su zauna a Masar kamar dā. Ni Ubangiji na faɗa.
27 “Ya bawana Yakubu, kada ka jitsoro,Kada ka firgita, ya Isra'ila.Gama zan cece ka daga ƙasa mainisa,Zan ceci zuriyarka daga ƙasarbautarsu.Yakubu zai komo, ya yi zamansa darai kwance,Ba wanda zai razanar da shi.
28 Ni Ubangiji na ce,Kada ka ji tsoro, ya bawanaYakubu,Gama ina tare da kai.Zan hallaka dukan sauran al'ummasarai inda na kora ka.Amma ba zan hallaka ka sarai ba.Zan hukunta ka yadda ya kamata,Ba zan bar ka ba hukunci ba.”