2 Domin haka lokaci yana zuwa,Sa'ad da zan sa mutanen garinRabba ta Ammon su ji busaryaƙi.Rabba za ta zama kufai,Za a ƙone ƙauyukanta da wuta,Sa'an nan Isra'ila zai mallakiwaɗanda suka mallake shi.Ni Ubangiji na faɗa.
3 “Ki yi kuka, ya Heshbon, gama Ai tazama kufai!Ku yi kuka, ku mutanen Rabba, kusa tufafin makoki.Ku yi gudu, kuna kai da kawowa acikin garuka,Gama za a kai Milkom bauta tare dafiristocinsa da wakilansa.
4 Me ya sa kuke taƙama daƙarfinku,Ƙarfinku da yake ƙarewa, ku mutanemarasa aminci?Kun dogara ga dukiyarku,Kuna cewa, ‘Wane ne zai iya gāba damu?’
5 Ga shi, zan kawo muku razana dagawaɗanda suke kewaye da ku,Za a kore ku, kowane mutum zaikama gabansa,Ba wanda zai tattara 'yan gudunhijira.Ni Ubangiji Allah Mai Rundunana faɗa.
6 “Amma daga baya zan saAmmonawa su wadata kuma,Ni Ubangiji na faɗa.”
7 Ga abin da Ubangiji Mai Rundunaya faɗa a kan Edom,“Ba hikima kuma a cikin Teman?Shawara ta lalace a wurin masubasira?Hikima ta lalace ne?
8 Ku mazaunan Dedan, ku juya, kugudu,Ku ɓuya cikin zurfafa,Gama zan kawo masifa a kan IsuwaA lokacin da zan hukunta shi,