3 “Ki yi kuka, ya Heshbon, gama Ai tazama kufai!Ku yi kuka, ku mutanen Rabba, kusa tufafin makoki.Ku yi gudu, kuna kai da kawowa acikin garuka,Gama za a kai Milkom bauta tare dafiristocinsa da wakilansa.
4 Me ya sa kuke taƙama daƙarfinku,Ƙarfinku da yake ƙarewa, ku mutanemarasa aminci?Kun dogara ga dukiyarku,Kuna cewa, ‘Wane ne zai iya gāba damu?’
5 Ga shi, zan kawo muku razana dagawaɗanda suke kewaye da ku,Za a kore ku, kowane mutum zaikama gabansa,Ba wanda zai tattara 'yan gudunhijira.Ni Ubangiji Allah Mai Rundunana faɗa.
6 “Amma daga baya zan saAmmonawa su wadata kuma,Ni Ubangiji na faɗa.”
7 Ga abin da Ubangiji Mai Rundunaya faɗa a kan Edom,“Ba hikima kuma a cikin Teman?Shawara ta lalace a wurin masubasira?Hikima ta lalace ne?
8 Ku mazaunan Dedan, ku juya, kugudu,Ku ɓuya cikin zurfafa,Gama zan kawo masifa a kan IsuwaA lokacin da zan hukunta shi,
9 Idan masu tsinkar 'ya'yan inabi sunzo wurinkaBa za su rage abin kala ba?Idan kuma ɓarayi sun zo da dare,Za su ɗauki iyakacin abin da suke sokurum.