26 “Gama an sami mugaye, a cikinjama'ata,Suna kwanto kamar masu kafaashibta.Sun ɗana tarko su kama mutane.
27 Kamar kwando cike da tsuntsaye,Haka nan gidajensu suke cike da cinamana,Don haka suka zama manya, sukasami dukiya.
28 Sun yi ƙiba, sun yi bul-bul,Ba su da haram a kan aikatamugunta,Ba su yi wa marayu shari'ar adalci,don kada su taimake su.A wajen shari'a ba su bin hakkinmatalauta.
29 “Ba zan hukunta su sabodawaɗannan abubuwa ba?Ba zan ɗaukar wa kaina fansa a kanal'umma irin wannan ba?
30 “Abin banmamaki da bantsoroYa faru a ƙasar.
31 Annabawa sun yi annabcin ƙarya,Firistoci kuma sun yi mulki da ikonkansu,Mutanena kuwa suna so haka!Amma sa'ad da ƙarshe ya zo, me zaku yi?”