16 Ku datse wa Babila mai shuka,Da mai yanka da lauje a lokacingirbi.Saboda takobin azzalumi,Kowa zai koma wurin mutanensa,Kowa kuma zai gudu zuwaƙasarsa.”
17 “Isra'ilawa kamar tumaki ne waɗanda zakuna suka bi su suna kora. Da farko dai Sarkin Assuriya ne ya cinye su. Yanzu kuwa Sarkin Babila, wato Nebukadnezzar, shi ne yake gaigayi ƙasusuwansu.
18 Saboda haka ni Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila na ce, zan yi wa Sarkin Babila da ƙasarsa hukunci, kamar yadda na hukunta Sarkin Assuriya.
19 Zan komar da Isra'ila a makiyayarsa, zai yi kiwo a Karmel da Bashan. Zai sami biyan bukatarsa a tsaunukan Ifraimu da na Gileyad.
20 Ni Ubangiji na ce sa'ad da lokacin nan ya yi za a nemi laifi da zunubi a cikin Isra'ila da Yahuza, amma ba za a samu ba, gama zan gafarta wa sauran da suka ragu.
21 “Ku haura ku fāɗa wa ƙasarMeratayim da mazaunan Fekod.Ku kashe, ku hallaka su sarai,Ku aikata dukan abin da na umarceku,Ni Ubangiji na faɗa.
22 Hargowar yaƙi tana cikin ƙasar,Da kuma babbar hallakarwa!